IQNA

Dubban Musulmi ne za su Halarci Arba'in Din Huseini A Ostriya

Bangaren Kasa Da Kasa: za a gudanar Juyayin cika kwanaki Arba'in da shahadar baban Abdalla Huseini (AS) a biranai daban-daban na Ostriya.
Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Barana cibiyar koyar Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa rahoton cewa: kungiyar yan shi'a a yammacin Ostriya sun fitar da bayanin cewa: a baya an gudanar da juyayin cika kwanaki arba'in da shahadar imam Huseini (AS) a biranai daban-daban a wannan kasa.A wannan bayani sun kara da cewa: Imam Huseini (AS) ba wai kawai ya kebantu day an shi'a ban e a'a lamarinsa ya shafi dukan musulmin duniya har ila yau ya shafi duk wani mai son adalci da laheri da tabbatar da gaskiya ga dukan bil adama ba tare da la'akari launin fatarsa ba ko addininsa ko yankin da ya fito ba. A wannan taro na juyayi an bukacin duk dan shi'a da musulmin da ke zaune a Ostriya day a halarci gurin taron juyayin da kungiyar ta bukaci da a gudanar da wajabai da ke kira da adamtaka da muhimman abubuwan day a sa Imam Huseini (AS) ya tashi gwagwarmaya.

362246