Bangaren Kasa da Kasa:Hauzar ilmi ta Najaf ta yi Allah wadai da matakin da Muhamad Algazzi mai shirya finafinai dan kasar Koweiti na shirya wasu jerin finafinai da a ciki zai wanke Ma'awiya bin Abi Sufiyan da Dansa Yazid daga zalumci da danniyar day a aikata kan iyalan gidan manzo (AS).
Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Aba' cibiyar koyar da Alkur'ani a Iran Iqna ta watsa labarin cewa: Muhamd Algazzi mai shirya fina-finai dan kasar Koweiti yana nan yana shirin kaddamar da wasu jerin fina-finan talbijin da a ciki zai wanke duk wani zalumci da danniya da Ma'awiya dan Abi Sufiyan Da Yazid Dan Ma'awiya suka aikata kan iyalan gidan manzon (AS) .kuma yin haka wani babban cin zarafi ne gay an shi'a da kuma iyalan gidan manzon da babu wani musulmi da yake kore irin zaluncin da aka aikata a kansu bayan rasuwar Manzon Allah (SWA).Bugu da kari yin irin wadannan fina-finai babu abin da sai haddasa illa Karin sabani da rashin fahimtar juna da rikici a tsakanin musulmi a daidai wannan lokaci da makiya musulmi ke kara cin zarafin addainin musulunci da musulmi a duniya ta fuskar zaner-zane da fina-finan batanci.
362718