Bangaren kasa da kasa: gwamnatin Britaniya tana cikin bincike kuma ta kai matakin karshe na sabon shiri karo na biyu na yakar musulmi da ke rayuwa a duniya baki daya.
Bayan ta nakalto daga majiyar watsa labarai ta Islam Online ,cibiyar kula da harkokin Alkur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: Jaridar Gwadiyan a fitowarta ta jiya a wata makala ta bada labarin cewa: gwamnatin Britaniya ta bullo da wani sabon shiri a karo na biyu na yaki da ta'addanci da hanyoyin yin haka a ci gaba da yakar duniyar musulmi ta hanyar fakewa da wannan manufa ta yaki da ta'addanci. A cikin wannan sabon shiri za a rika bayyana bakaken kalaman batanci kan musulmi da gwamnatocinsu ba tare da shamaki ba kuma muslman da sojojin Amerika suka kasha a Iraki da Afganistan ba za a yi suka da Allah wadai kan hakan bad a dai sauran matsaloli makamantan haka da danne hakkokin musulmi a duniya.
365753