Bangaren kasa da kasa: Poproma Benedict na 16 zai kai wata ziyara a kasar Jordan, inda zai gana da jagororin musulmi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa; a ziyarar da Benedict din zai kai Jordan, zai gana da wasu malaman addinin musulunci ne a masallacin (Shan Hossain) da ke birnin Aman fadar mulkin kasar, da nufin kara fadada dangantaka tsakanin mabiya addinan musulunci da kiristanci a duniya , musamman a yankin gabas ta tsakiya.
A cikin shekara ta 2006 ce Benedict ya bayyana addinin muslunci a matsayin wani addini da ke kira zuwa ga tashin hankali, inda a halin yanzu yake kokarin nuna kyakkyawar niyarsa ta kyautata danganta tsakaninsa da musulmi.
366010