IQNA

An Bude Kasuwar Baje Koli Ta Kayan Tarihin Musulunci A Kasar Rasha

Bangaren kasa da kasa: An fara gudanar da wata kasuwar baje kolin kayan tarihin musulunci a kusa da fadar Kirmilin ta kasar Rasha da ke birnin Moscow fadar mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Hadaddiyar Daular Larabawa cewa; an fara gudanar da kasuwar baje kolin ne wadda ma'aikatar kula da al'adu ta kasar Kuwait ta shirya ne tare da halartar ministan sadarwa na kasar Kuwait din (Sabah Khalid Sabah) tare da wsu jami'an gwamnatin Rasha, inda aka baje kayayyakin tarihi da suke komawa ga tarihin addinin musulunci, da hakan ya hada da takubba, da kasakai, garkuwa, da suka duwatsu masu daraja da aka yi zane kansu, da tarihinsu ke komawa zuwa daruruwan shekaru , wasu kuma sama da shekaru dubu daya da suka gabata.
Bayan kammala taron baje kolin za a kwashe kayan zuwa gidan tarihi da ke garin Petersburg da ke kudancin Rasha.

367087