IQNA

Wasika ta musamman a watan Safar A shafin Cibiyar Musulunci A Britaniya

Bangaren Abubuwan da Aka amince: Shafin sadarwa na cibiyar musulunci a Britaniya ce ta kaddamar da wasika musamman ta watan safar kan ranekun addini.
Cibiyar kula da harkokin alkur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: wannan wasika ta kumshi korar manzon Allah (SWA) shahadar imam Hasan (AS) da imam Rida (AS) da kuma hadisan rayuwar masu ziyarar markadin Imam Huseini (AS) a karbala. A bangaren day a shafi rayuwar manzon har zuwa korarsa da bankwana da wannan duniya da yadda yayi hijira da gudanar da hajin bankwana da abubuwa da suka wakana a lokacin na bayyana wasiyinsa a tsakiyar Hamada a wata mararraba ta Gadir Khum < sai kuma lokacin rashin lafiyarsa da yin bankwana da wannan duniya da abubuwan da suka biyo baya.Yayinda wasikar ta tabo kyawawan dabi'un imam Hasan (AS) ta yi bayani dalla-dalla kan halaryarsa da yadda ya juriya kan abubuwa da suka faru kansa .

367115