Bangaren zamantakewa: Za a gudanar da taron tsoffin dalibai musulmi da suka kammala karatu a jami'oin kasar Birtaniya a birnin Tehran.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; wannan taro zai dubi ne kan irin gudunmawar da tsoffin daliban za su iya bayarwa wajen yada al'adu na addinin musulunci tsakanin al'ummomin turai, musamman ganin cewa suna da masaniya kan irin al'adun turai musamman ma Birtaniya, da kuma bayar da gudunmawa wajen taka birki ga irin parpagandar da ake yi a kasashen turai marassa tushe kan addinin musulunci, da nufin nisantar da al'ummomin wannan nahiya daga fahimtar addinin musulunci da kuma kyakkyawar koyarwarsa.
Gudanar da wannan taro na daya cikin manufifin jagoran juyin juya halin musulunci a Iran (Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei) na kara wayar da kan dalibai da suka yi karatu a turai dangane da yadda za su yada manufofin addinin musulunci a kasashen ketare.
368258