Bangare na kasa da kasa: An gudanar da taron tunawa da zagayowar ranar wafatin manzon Allah (SAW) da Imam Hassan (AS) a garin Rawalpandi na kasar Pakistan.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar (The News) da ake bugawa a kasar Pakistan cewa; kungiyar mabiya mazhabar shi'a ta birnin Rawalpandi ce ta shirya gudanar da taron, wanda ya samu halartar malaman addinin muslunci na mabiya mazhabar shi'a da kuma malamam sunna, gami da masana daga sassa daban-daban na kasar Pakistan.
Wani babban malamin addini na kasar Pakistan da ya halarci taron (Allamah Sayyid Zakir Hussain Shah) ya gabatar da jawabi a wurin, inda ya bayyana Imam Hassan (AS) a matsayin wani mutum da ke misilta ayyukan manzon Allah a aikace, kuma dukkanin sirarsa tana tunatar da mutane sirar manzon Allah ce.
369002