IQNA

Al-Tuwaijari Ya Kira Yi Musulmi Da Su Motsa Don Kubutar Da Quds

Bangaren kasa da kasa: Sakataren kungiyar yada al'adu da koyarwa irin ta Isalama (Abdolaziz Osman Al-tuwaijari) ya kirayi dukkanin al'ummar musulmi na duniya da su safke nauyin da ya rataya kansu na kubutar da masallacin Quds.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labarai na SANA cewa; sakataren kungiyar yada al'adu da koyarwa irin ta ddinin musulunci Abdolaziz Osman Al-tuwaijari ya bayyana matakin da Isra'ila ta dauka na kokarin yahudantar da birnin Quds da cewa mataki mai matukar hadari, musamman ma idan aka yi la'akari da yunkurin da wasu yahudawa masu tsattsuran ra'ayi ke yin a rushe masallacin Quds mai alfarma, ta hanyar gina wasu manyan ramuka a karkashin masallacin, ya ce ya zama wajibi kan al'ummar msulmi na duniya da su kubutar da masallacin Quds mai alfarma daga barazanar rushewa da yake fuskanta daga yahudawan sahyuniya.

369881