IQNA

Masu Ziyarar Wurare Masu Tsarki Su Aikata Duk Abin Da Zai Kara Hada Kan Musulmi

Bangaren zamantakewa: Wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci a kasar Saudiyya Ayatollah Mohammad Mohammadi Rai-Shahri, ya kirayi masu ziyartar wurare masu tsarki da su aikata duk wani abin da zai kawo hadin kai tsakanin musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet mallakin wakilin jagoran juyin juya halin Musulunci a kasa mai tsaki Ayatollah Mohammad Mohammadi Rai-Shahri cewa; masu gudanar da ayyukan ziyara a kasa mai tsarki a lokutan ayyukan Hajji da Umrah, su yi kokari su kiyaye hadin kan al'ummar musulmi, ta hanyar barin duk abin da zai iya kawo rarraba da tsakanin musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa masu gudanar da ayyukan ziyara a wurare masu tsarki musamman daga jamhuriyar Musulunci ta Iran, suna wakiltar babbar kasa ce ta musulmi, wadda take taka rawa wajen samar da kyakkyawan hadin kai tsakanin wannan al'umma mai daraja, a kan haka, malamin ya kirayi mutanen Iran musamman da su kiyaye duk abin da zai kara hada kan al'ummar musulmi na duniya a lokacin gudanar da ayyukan ziyararsu a kasa mai tsarki.

370760