IQNA

Iraki Za Ta Iya Taka Muhimmiyar Rawa A Tsakanin Kasashen Musulmi

Bangaren siyasa: A lokacin da yake ganawa da mataimakin shugaban kasar Iraki Shugaban majalisar kwararru ta Iran ya bayyana cewa Iraki za ta iya taka muhimmiyar rawa a tsakanin kasashen musulmi.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci cewa; shugaban majalisar Ayatollah hashemi Rafsanjani a wata ziyara da yake kaiwa kasar Iraki ya gana mataimakin shugaban kasar Adel Abdolmahdi.
Hashemi Rafsanjani ya ce babbar manufar ziyararsa a Iraki ita ce kara kara fada danganataka tsakanin Iran da Iraki, tare da taimaka ma Iraki ta bangarori da dama, da kuma ganawa da manyan malaman addini na kasar, da kuma manyan jami'an gwamnati. Ya ce Iraki kasa mai matukar muhimmanci a tsakanin kasashen musulmi, kuma a tsakanin kasashen larabawa da na musulmi za ta iya taka gagarumar rawa.
Ya ce Iran a shirye take ta taimaka ma Iraki da ta fsukoki da dama daga irin masaniyar da take da ita a halin yanzu kan harkokin tattalin arziki, al'adu, kasuwanci da dai sauransu.

371403