Bangaren rahoto: Ruhullah Ramanzanpoor Karimi tsahon mamba a majalisar kwararru masu zabar jagora a Iran, ya bayyana Imam Khomeni (RA) da cewa babban masanin akidar markisanci ne.
Kamfanin dillancin labaran Ikna da daga birnin Qom ya habarta cewa; an gudanar da wani taron dangane da juyin juya halin msulunci a Iran a jami'ar Qom, inda wani babban malami (jalaluddin Farisi) ya gabatar da jawabai dangane da irin ci gaban da Iran ta samu bayan samun nasarar juyin juya halin musulunci karkashin jagorancin marigayi Imam Khomeni, ya ce daga cikin irin ci gaban da Iran ta samu albarkacin juyin juya halin musulunci har da ci gaban ilimi, da fasaha da kere-kere da inganta masana'antu, kamar yadda Iran ta zama abun buga misali da ita wajen gudanar da ayyuka na nukiya domin ayyukan farar hula, haka nan ta fuskacin ilimomin addinin da sanin zamantakewar jama'a.
Ya ce duk wannan ya samu ne sakamakon namijin kokarin da Imam Khomeni (RA) ya yi, wanda ya bayyana shi da cewa babban masanin akidar markisanci ne.
371943