IQNA

Za A Samar Da Wata Hanyar Bayar Da Shawarwari Ga Dalibai Ta Wayar Tarho

Bangaren Internet: Shugaban bangaren da ke kula da tarbiya da bayar da shawarwari ga dalibai a cibiyar ilimi ta Hauza da ke birnin Qom, ya bayyana cewa za a samara da wata hanya da za a iya zantawa da dalibai kai tsaye ta wayar tarho domin ba su shawarwari.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga cibiyar ilimi ta Hauza da ke birnin Qom cewa; shugaban bangaren da ke kula da tarbiya da bayar da shawarwari ga daliban da ke karatu a cibiyar (Reza Amiri) yabayyana cewa; nan ba da jimawa ba za a samara da wata hanya wadda za a iya tuntubar dalibai ko kuma su tuntubi bangare da ke kula da tarbiya da shawari kai tsaye, domin sauraron matsalolinsu tare da ba shawarwari kai tsaye, ya ce hanyar da za a yi amfani da ita baki daya aiki ne na na'ura mai kwakwalwa, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da za a aiwatar da irin wannan a fadin kasar.
Ya kara da cewa hanyar za ta sawake wa dalibai da dama wajen neman shawara kan lamurran da suka shafi rayuwarsu ta dalibta.

372199