Bangaren siyasa da zamantakewa: Za a gina babbar cibiyar ilimi ta Hauza a garin Jalafa, da za ta dauki dalibai daga kasashen duniya musamman mata daga cikinsu.
A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran Ikna, babban limamin garin Jalfa ya bayyana cewa; bisa la'akari da kokarin da mata suka nuna a dukkanin fagage na karatun hauza, an yanke shawarar gina babbar cibiyar ilimi ta hauza a garin na jalfa mai suna fatimat Zahra, wadda za ta dauki dalibai daga sassa daban-daban na duniya domin bas u ilimin addini.
A bangare guda kuma ya yaba wa jami'ai da suke fadi tashin ganin an kara fadada ilimin addinin tare yada shi a ko'ina cikin fadin duniya ta hanyar gina cibiyoyin ilimin addini na Hauza, wanda hakan a cewarsa yana taka gagarumar wajen ilmantar da shiryar da al'ummomi, musamman matasa daga cikinsu, wadanda suke bukatar shiryarwa a kowane, wanda kuma shiryuwarsu na nufin shiryuwar al'umma ne, domin sun e manyan gobe.
373702