Bangaren siyasa da zamantakewa: Musulunci ya yarda ne kawai a yi amfani da hankali da sanin ya kamata wajen warware matsalolin duniya.
A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran Ikna da shugaban cibiyar kula da tattaunawa tsakanin addinai, ya bayyana cewa a kowane lokaci Musulunci yana tafiya dai dai da hankali, kamar yadda dukkanin hukunce-hukuncensa suka yi dai dai da hankali da fitira ta dan adam, ya ce idan muka dubi yadda Musulunci yake warware mas'aloli da suka shafi rayuwar dan adam ta zamantakewa, a lokacin zamu fahimci cewa Musulunci addini ne na hankali da fitira. Ya kara da cewa addinin Musulunci yana amsa tambayoyi da suka shige wa dan adam a cikinduhu, wanda rashin sanin takamaimar amsar Musulunci ya sanya wasu shiga cikin dimuwa a kan akidoji da suke musunta samur ubangiji.
376009