IQNA

Kungiyar Malumman Hauza A Shiraz Ta Yi Allah Wadai Da Abun Da Ya Faru A Saudiya A Baya-bayan Nan

Bangaren siyasa da zamantakewa: kungiyar hadin gwiwar malumman hauza a shiraz sun yi Allah wadai da abin da ya faru a baya-bayan nan a Saudiya da Wahabiyawa sun ci mutuncin masu ziyara a Makabartar Manzo (SWA).
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta fitar da labarin cewa; cikin bacin rai da bakin cikin abin da ya faru a baya-bayan yan a Saudiya na cin mutuncin masu ziyara da Wahabiyawa suka yi a wannan gurin mai albarka da daukakana makwancin ma'aikin Allah Muhammadu dan Abdullah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da cewa: abin Allah wadai ne a dai dai wannan lokaci a samu wani da zai ci mutuncin wani musulmi a wannan guri na ma'aiki abin girmamawa.

375795