Bangaren kasa da kasa: Gwamnatin kasar Somalia tat a amince da batun gudanar da tsarin shari'ar musulunci a cikin dokokin kasar .
Kamfanin dillancin labaran Iknaya nakalto daga kamfanin dillancin labaran (AFP) na kasar Faransa cewa; Ministan yada labarai na kasar Somalia (Farhan Ali Mahmud) ya bayyana cewa; dukkanin 'yan majalisar dokokin kasar sun yi dogon nazari dangane da batun saka tsarin shari'ar musulunci a cikin tsarin shari'ar kasar, inda daga karshe dai suka amince kan cewa za a saka tsarin shari'ar musulunci a cikin tsarin shari'ar kasar, bisa la'akari da cewa dukkanin al'ummar kasar Somalia mabiya addinin musulunci ne.
A nasa bangaren sabon shugaban kasar ta Somalia Sheikh Sharif Ahmad, ya nuna matukar gamsuwarsa kan hakan, ya kuma yi kira da a fara aiwatar da hakan ba tare da wani bata lokaci ba.
376471