IQNA

An Gudanar Da Zaman Tantance Mahangar Malaman Tafsiri

Bangaren fikra: An gudanar da wani zama domin tantance mahangar malaman tafsiri kan wasu muhimman batutuwa da suka zo cikin kur’ani, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irinsa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gudanar da wani zama domin tantance mahangar malaman tafsiri kan wasu muhimman batutuwa da suka zo cikin kur’ani, wanda kuma wannan shi ne karo na biyu da ake gudanar da irinsa, wanda kuma bangaren kula da harkokin tafsirin kur’ani na Ikna ne ya shirya gudanar da zaman a karo na biyu, inda aka gayyaci manyan malamai musamman masana kan kar’ani domin tattauna wasu muhimman batutuwa da masu tafsirai suka bayyana mahangarsu akansu, domin fayyace mahangar kowane daga cikinsu. A bangare guda kuma zaman ya tabo batun ijtihadi a cikin tafsirin kur’ani, da kuma dalilan safkar ayoyi gami da hadisai da ruwayoyi da suke tabbatar da dalilin safkar aya, da dai sauran batutuwa da suke da dangantaka da hanyoyin tabbatar da sahihancin bayani ko tafsirin aya da dalilan safkarta. Rahoton ya ce malaman sun yi bahasi mai zurfi, kuma za a ci gaba da gudanar da hakan domin fayyace mahangar malaman tafsiri kan muhimman batutuwa.

378995