Bangaren rahoto: Malaman addinin yahudanci bayan bayyanar addinin musulunci a hijaz, sun yi iyakacin kokarinsu wajen gurbata addinin musulunci ko kawar da shi baki daya, bayan da hakan ya ci tura sai suka hada baki da kuraishawa wajen kulla munafunci domin cutar da mabiya addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga Hossein Kasim Najad cewa; malaman addinin yahudanci bayan bayyanar addinin musulunci a hijaz, sun yi iyakacin kokarinsu wajen gurbata addinin musulunci ko kawar da shi baki daya, bayan da hakan ya ci tura sai suka hada baki da kuraishawa wajen kulla munafunci domin cutar da mabiya addinin musulunci.Ya ci gaba da cewa ya zo a cikin tarihi bisa madogara mai tushe cewa; wani bayahude mai suna Sha'un Yahudi, ya shiga addinin kiristanci, amma kafin lokacin annabi Isa ya bayyana masa yana cewa me ya sanya kuke cutar da ni haka, wannan ya yi masa tasiri matuka, inda ya fahimci cewa addinin annabi Isa shi ne gaskiya, bai yi wata-wata ba wajen komawa kan tafarkin shari'a irin na annabi Isa. Malamin ya ci gaba da cewa hakika yahudawa sun yi tasiri matuka wajen juya akalar addinin kiristanci daga hakikanin koyarwa irin ta annabi Isa, domin kawai su kawar da mabiya addinin kiristanci daga hakikanin koyarwarsa.
380652