IQNA

Nazari Kan Ma'anar Ceto A Mahangar Kur'ani

Bangaren fikira da ilimi: Batun ceto na daya daga cikin batutuwa da wasu mazhabobin musulunci suka samu sabani a kansu, duk da cewa mas'ala ce da kur'ani ya yi bayani kanta a cikin wasu ayoyi bayyanannu.
A cikin wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Ikna reshen Lardin Azarbaijan ta yamma ya hada dangane da mahangar malamai da ya zanta da su kan batun ceto, sun bayyana cewa; wannan wani batu ne wanda yana daya daga cikin batutuwa da wasu mazhabobin musulunci suka samu sabani a kansu, duk da cewa mas'ala ce da kur'ani ya yi bayani kanta a cikin wasu ayoyi bayyanannu. Malaman sun yi Karin haske kan cewa akasarin musulmi sun yarda da batun ceto bisa dalilai na kur'ani da hadisan ma'aki (SAW) amma wasu daga cikin musulmi da suke bin akidar wahabinyaci ba su yarda da ma'anar ayoyin ceto gami da hadisan da suka yi bayani kan hakan ba, musamman ma dai ceton limaman gidan manzon Allah(SAW) inda suke bayyana hakan da cewa ba ma kawai ba su amince da shi ba ne a shirka ce kai tsaye a mahangarsu, duk da cewa ba mabiya tafarkin iyalan gidan manzo ne kawai suke da imani da ceto ba,a a har ma da manyan malaman sunna da suka gabata.

381466