IQNA

An Fitar Da Makalolin Taron Kasa Da Kasa Kan Ma'aiki (SAW) A Thailand

Bangaren al'adu da fasaha: An buga tare da yada littafin da ke dauke da dukkanin makalolin da aka gabatar a taron kasa da kasa da aka gudanar kan matsayin manzon Allah (SAW) a birnin Bankuk na kasar Thailand.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; Bangaren kula da al'adu tare da yada koyarwar musulunci na kasar Iran ya buga tare da yada littafin da ke dauke da dukkanin makalolin da aka gabatar a taron kasa da kasa da aka gudanar kan matsayin manzon Allah (SAW) a birnin Bankuk na kasar Thailand. Rahoton ya kara da cewa babbar manufar buga tare da yada wannan littafi ita ce kara wayar da kan al'ummar musulmin kasar Thailand wajen sanin matsayin ma'aiki da kuma koyarwarsa, da kuma yadda ya kamata kowane musulmi ya yi da manzon Allah (SAW) a cikin harkokin rayuwarsa gaba daya, kama daga rayuwarsa da sauran al'ummomi da yake da banbancin akidar addini da su, wato wadanda ba musulmi ba, har zuwa rayuwa tsakaninsa da sauran 'yan uwansa musulmi, da kuma rayuwa ta zamnatakewa tsakaninsa da iyalansa da danginsa da dai sauransu. An tattara makalolin da manyan malamai dam asana suka gabatar ne a wajen taron na kasa da kasa da aka gudanar a birnin Bankuk fadar mulkin kasar Thailand dangane da matsayin ma'aiki, inda aka mayar da su littafi.


382120