IQNA

An Kai Littafan Musulunci A Kasuwar Baje Kolin Littafai A Thailand

Bangaren al'adu da fasaha: An baje kolin wasu daga cikin littafan addini a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a karo na bakwai a birnin Bankuk na kasar Thailand.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; An kai wasu daga cikin littafan addini a kasuwar baje kolin littafai ta duniya da ake gudanarwa a karo na bakwai a birnin Bankuk na kasar Thailand, daga cikin irin littafan da aka kai kuwa har da littafan da ke bayar da haske kan muhimman lamurran da ya kamata musulmi ya sani dangane da addininsa, da kuma tarihin juyin juya halin musulunci a Iran, gami da tarihin rayuwar Imam Khomein da gwagwarmayarsa da dai sauransu.
Wannan dai shi ne karo na bakwai da ake gudanar da irin wannan kasuwar baje kolin littafai a kasar Thailand, kuma za a kammala baje kolin a ranar litinin mai zuwa. Wannan kasuwar baje koli ta samu halartar wakilan cibiyoyi 450 da ke bugawa tare da yada littafai daga sassa daban-daban na duniya.

382119