Bangaren al'adu da fasaha: An buga tare da yada littafin nan mai suna littafin tsarkaka, wanda cibiyar ahlul bait ta duniya ce ta dauki nauyin fassara shi a cikin harshen Bolgaria.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya habarta cewa; an buga tare da yada littafin nan mai suna littafin tsarkaka, wanda cibiyar ahlul bait ta duniya ce ta dauki nauyin fassara shi a cikin harshen Bolgaria. Rahoto ya kara da cewa wannan littafi da aka fassara yana da shafuka 54, kamar yadda kuma ya kunshi kissishi kan rayuwar manzon Allah (SAW) da Imam Ali (AS) da kuma Fatimah Al-zahra (AS) wanda kuma an tsara shi ne domin amfanuwar matasa, wadanda suke karatu a makarantu da kuma yin nazari, yanzu hakan an buga kwafi dubu daya na wannan littafi.
382438