Bangaren kasa da kasa: Daga ranar litinin 17 ga watan farvardin 6 ga watan Apirilu za a fara gudanar da tarukan makon wayar da kai manufofin addinin musulunci a jami'ar Harward, da nufin sanar da wadanda ba musulmi ba hakikanin manufar addini dangane da rayuwar dan adam.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin interne mallakin kungiyar dalibai musulmi na jami'ar harward cewa; Daga ranar litinin 6 ga watan Apirilu za a fara gudanar da tarukan makon wayar da kai manufofin addinin musulunci a jami'ar, da nufin sanar da wadanda ba musulmi ba hakikanin manufar addinin musulunci da koyarwarsa dangane da rayuwar dan adam. Kungiyar za ta shirya taron ne wanda zai kwashe tsawon kwanaki biyar ana gudanar da shi, da nufin nuna hakikanin surar addini ga sauran dalibai wadanda ba mabiya addinin musulunci neb a, domin kawar da shamakin da aka saka day a kange su daga fahimtar addinin musulunci, maimakon hakan ana nuna musu addainin musulunci a matsayin wani addini ne na tashin hankali da rashin tausayi ballantana sanin manufa. A yayin gudanar da wadan taruka za a gabatar da laccoci, da kuma saka azuzuwan tattaunawa tare da amsa tambayoyi, kamar yadda za a baje kolin wasu kayyakin musulunci, gami da littafai da aka fassara a cikin yaruka 10 da suke bayani kan addinin musulunci.
382952