Bangaren fasaha: Ma'aikatar kula da al'adu ta kasar Iran ta sha alwashin yin aiki dari busa dari da kirarin wannan shekara na tsuke bakin aljihu da kuma nisantar duk wasu ayyyka na almubazzaranci kamar dai yadda jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya saka wa shekarar suna.
Kammfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren hulda da jama'a na ma'aikatar kula da al'adu ta Iran cewa; ministan ma'aikatar Mohammad Hossein Saffar Herandi ya bayyana cewa ma'aikatarsa ta sha alwashin yin aiki dari bisa dari da kirarin wannan shekara na tsuke bakin aljihu da kuma nisantar duk wasu ayyyka na almubazzaranci kamar dai yadda jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya saka wa shekarar suna. Mohammad Hossein Saffar Herandi ya bayyana hakan ne a gaban daruruwan ma'aikatansa a babban ginin ma'aikatar da ke birnin Tehran. Ya ci gaba da cewa ya kamata dukkanin ma'aikata da ma sauran al'ummar Iran su fahimci irin muhimmancin da ke tattare da saka wannan suna da jagoran juyin juya halin musulunci ya saka wa wannan shekara, kuma hakan ba wai kawai a suna ya tsaya ba, a a hakan na bukatar aiki ne daga dukkanin al'ummar Iran, domin maslaha ce ga kasa baki daya, a kan haka ce ma'aikatarsa ta sha alwashin yin aiki da manufofin wannan kirari na sabuwar shekarar bana.
383040