Bangaren nazari: Littafin day a kumshi wasiku hudu a lokacin Gaiba da sheikh Mufid ya rubuta day a kumshi gaibar Imam Zaman (AS) musamman kan Tsayuwarsa (AS) da kuma amsa kan shubuhar imamancinsa suna daga cikin abubuwan da littafin ya kumsa.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta kawo labarin cewa: littafin wasiku hudu kan Gaiba da sheikh Mufid ya rubuta Muhammad bin Muhammad bin Na'aman Bagadadi daya daga cikin manyan malummai da suka yi fice ta fuskar Fikuhu a tsakanin malumman Shi'a a karni na biyar Hijira ya bayyana da bada amsa kan Gaibar Imam Mahdi (A) da kuma sauran amsoshi kan imamancinsa. Duk wani littafi da za a rubuta ba shi da kima da matsayi a gurin yan shi'a kamar litafi da zai yi Magana da bayani kan gaiba da imamancin Imam Mahdi (A) . A lokacin zamanin sheikh Mufid wannan yana daga cikin dalilin day a say a rubuta wannan littafi.
382854