Bangaren kasa da kasa: Sakataren kungiyar bunkasa ilimi da al'adun musulunci Abdulaziz Osman Al-tuwaijari, ya yi kira da a ci gaba da gudanar da tattaunawa kan al'adu da addinai, domin kara samar da fahimtar juna tsakanin al'ummomin duniya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; babban sakataren kungiyar bunkasa ilimi da al'adun musulunci Abdulaziz Osman Al-tuwaijari, ya yi kira da a ci gaba da gudanar da tattaunawa kan al'adu da addinai, domin kara samar da fahimtar juna tsakanin al'ummomin duniya. Al-tuwaijari ya yi wannan kira ne a wajen taron tattaunawar al'adu da aka gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya, inda ya bayyana cewa ci gaba da tattaunawar shi ne zai bayar da dammar samun fahimtar juna tsakanin al'ummomi masu banbancin al'adu da ma addinai a matsayinsu na 'yan adam, ya kara da cewa babban abin da zai kawo zaman lafiya a duniya baki daya bai wuce fahimtar juna da sulhu ba, tare da yin aiki da dokoki na kasa da kasa ba tare da nuna bangaranci kan wata al'umma ko addini ba. Ya ce wannan nauyi ne da rataya kan shugabannin addinai da ma shugabannin gwamnatoci gami da suka al'ummomi kansu.
384296