Bangaren kasa da kasa: Kungiyar bunkasa ilmomi da al'adun addinin musulunci za ta halarci wani taro da aka shirya gudanarwa a kasar Morocco, dangane da mahangar marubutan Amurka kan rayuwar ma'aiki (SAW).
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na ISESCO cewa; kungiyar bunkasa ilmomi da al'adun addinin musulunci za ta halarci wani taro da aka shirya gudanarwa a birnin Fas na kasar Morocco, dangane da mahangar marubutan Amurka kan rayuwar ma'aiki (SAW) bayanin ya ci gaba da cewa jami'ar adabi da ilimin sanin halayyar dan adam ta kasar Morocco da kuma hadin gwiwar ma'aikatar kula harkokin addini ta kasar za su dauki nauyin gudanar da wannan taro. Masana daga kasashe daban-daban na duniya ne za su halarci taron, da suka hada da kasashen Saudiyya, Masar, Hadaddiyar daular larabawa, Oman, Algeria, Malasia, Amurka da kuma mai masafkin baki Morocco, inda za su yi bahasi kan mahangar marubutan Amurka dangane da rayuwar ma'aiki (SAW)
384812