Bangaren kasa da kasa: Kotun kasar Masar ta dakatar da buga wata mujalla a kasar bayan da ta buga wata waka da ke cin zarafin addinin musulunci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga majiyar jami'ar Alazhar ta kasar Masar cewa; wata kotu a kasar ta Masar ta dakatar da buga wata mujalla a kasar bayan da ta buga wata waka da ke cin zarafin addinin musulunci. Kotun dai ta dauki wannan mataki ne bayan jami'ar alazhar ta shigar da kara kan wannan mujalla, dangane da wakar da ta buga, inda malaman jami'ar suka yi Allawadai da hakan tare da bayyana shi da cewa cin zarafin addini ne da musulmi ba za su taba amincewa da shi, inda suka nemi kotu da ta yanke hukunci dake haramta ci gaba da buga wannan mujalla domin ladaftar da ita.
385673