IQNA

Musulmin Italia Sun Yi Addu'o'i Ga Wadanda Girgizar Kasa Ta Shafa

Bangaren kasa da kasa: Mabiya addinin musulunci sun gudanar da addu'o'i a dukkanin masallatan kasar ga wadanda girgizar kasa ta shafa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Italia cewa; mabiya addinin musulunci sun gudanar da addu'o'i a dukkanin masallatan kasar ga wadanda girgizar kasa ta shafa a kasar. Kamfanin dillancin labaran kasar ta Italia (AKI) ya kara da cewa; babban malamin addinin musulunci na kasar Italia Abdullahi Ridwan ya kirayi dukkanin musulmin kasar da su gudanar da addu'o'i ga wadanda suka girgizar kasa ta shafa, da hakan ya hada da masallatansu na juma'a da ma sauran wurare da musulmi suke tarukansu na ibada. Rahoton ya kara da cewa bisa wannan kira a ranar juma'a dukkanin musulmin kasar Italia sun gudanar da addu'o'i a masallatan juma'a da ke fadin kasar, na nufin neman sauki ga wadanda suka samu raunuka ga wadanda girgizar kasa ta shafa kai tsaye.

385652