IQNA

Dole Ne Musulmin Faransa Su Shiga Cikin Harkokin Zamantakewa A Dama Da Su

Bangaren kasa da kasa: Daya daga cikin malaman jami'a a kasar Faransa (Tarik Ramedan) ya kirayi musulmin kasar Faransa da su shiga a dama da su a cikin harkokin zamantakewar al'ummar kasar a dama da su.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa (AFP) cewa; fitaccen malamin falsafar nan kasar Faransa kuma malaman jami'a a kasar (Tarik Ramedan) ya kirayi musulmin kasar Faransa da su shiga a dama da su a cikin harkokin zamantakewar al'ummar kasar a dama da su. Malamin ya bayyana hakan ne jiya a wajen wani taro da musulmin kasar Faransa suka gunar, wanda shi ne irinsa na ashirin da shida da suke gudanarwa sau daya a kowace shekara.
Ya ce musulmi suna da rawar da za su iya takawa a cikin harkokin rayuwar zamantakewa a tsakanin al'ummomin kasashen turai, musamman ma musulmin Faransa, wadanda bai kamata su zama saniyar ware ba a cikin harkokin yau da kullum a kasar.

386672