IQNA

An Gudanar Da Sallar Jam'I 600 A Haramin Imam Rida(AS)

Mai kula da haramin Imam Rida ne Ya bayyana cewa; A cikin kwanaki 13 na shiga sabuwar shekara a Haramin Imam Rida (AS) An gudanar da sallar jam'I 600.
Malam Jalali Huseini mai kula da ofishin yada labarai da kula da abubuwa na musamman a Haramin Imam Rida (AS) a watan tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ya bayyana cewa; bayan gudanar da sallar jam'I 600 a cikin kwanaki sha uku na shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiya an kuma gudanar da zama na musamman sau 78 da kuma jawabai da suka shafi muhimmancin hakuri da juriya,Sanin Imami,Alamomin Zuhuri,Siffofin Manzon Allah (SWA) suna daga cikin maudu'an da aka gabatar da jawabai a kansu.

386871