IQNA

An Buga Makala Kan Yakin Kwanaki 22 Ranar Isra'ila Kan Palasdinawa A cikin Wallafawar Hanyar rayuwa Senegal

Bangaren ilimi da nazari: Makalar yakin kwanaki 22 ranar Isra'ila kan Palasdinawa nasar ko kasa cin nasara? Da Muhammad Ali Basiri ma'aikacin ofishin yada al'adun Iran a kasar Senegal ya rubuta a cikin littafin day a wallafa mai sunan hanyar rayuwa a Senegal.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta watsa rahoton cewa: Basiri ma'aikacin ofishin da ke kula da yada al'adun Iran a kasar Senegal a cikin wannan makala ya yi nuni da harin ta'addanci da nuna kiyayya da makiya yahudawan sahayoniya a gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kaddamar na rashin tausayi kan al'ummar Palasdinu a tsawon kwanaki ashirin da biyu a jeer a kokarin da suka bayyana na ganin bayan kungiyar Hamas,bugu da kari ya yi nuni day akin kwanaki 33 da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kaddamar kan al'ummar Labanon a kokarinsu na ganin karshen kungiyar Hizbullah inda a ya kawo dalilai guda goma na asalin kasa cin nasarar haramtacciyar kasar Isra'ila ta dukan fuskoki da ya hada tsaro,tattalin arziki da siyasa da kuma martabarta a idon duniya da al'ummomi.

387095