IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Matsayin Ilimi A Musulunci

Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da taro kan matsayin ilimi a addinin musulunci, wanda cibiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci ta kasar Algeria ta shirya gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Elmojahid cewa; za a gudanar da taro kan matsayin ilimi a addinin musulunci, wanda cibiyar kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci ta kasar Algeria ta shirya gudanarwa. Sheikh Muhammad Al-akhal, mataimakin kungiyar malaman addinin musulunci ta kasar Algeria ya bayyana cewa; za a gudanar da wannan taron domin yin dubi kan mahangar musulunci dangane da ilimi da kuma muhimmancinsa a cikin rayuwar dan adam, a rayuwa ta zamantakewa har zuwa bangaren siyasa, da kuma yadda musulunci yake karfafa gwiwar dan adam wajen gudanar da bincike domin ci gaban rayuwa. Cibiyar kula da al'adu da ilimin addinin musulunci ta kasar Algeria ce ta shirya gudanar da wannan taro a karo na farko, wanda kuma hakan bangare ne na ayyukan da take gudanarwa a kasar.

387573