IQNA

An baje Kolin Littafan Addinin Musulunci A Jami'ar Indiana

Bangaren kasa da kasa: Ana ci gaba da baje kolin littafan addinin musulunci a jami'ar Indiana ta kasar Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet (IUPress)cewa; an ci gaba da baje kolin littafan addinin musulunci a babban dakin baje kayan tarihi na jami'ar Indiana da ke jahar Indiana a kasar Amurka, bayanin ya ci gaba da cewa an saka kimanin littafan musulunci guda 50 a baje kolin, wadanda tarihinsu yake komawa zuwa ga karni na 9, kamar yadda aka baje kolin wasu kayan tarihi na addinin musulunci, wadanda suma tarihinsu yana komawa zuwa ga daruruwan shekaru, daga ciki kuwa har da wasu kayayyakin tarihi na daular Usmaniya, da daular Magol, gami da wasu takardu da aka samu da ke dauke wasu rubuce-rubuce na addinin musulunci, wadanda su ma suna cikin abubuwan da aka baje a dakin tarihi na jami'ar Indiana, za a ci gaba da gudanar da wannan baje koli har zuwa makonni uku a nan gaba.


387018