IQNA

An Watsa Littafin Day a Kumshi Istifta.at Na Ayatullahi Al'uzma Bujurdi

Bangaren al'adu da fasaha: Jikan Ayatullah al'uzma Bujurdi ya fitar da wani littafi da ya kumshi amsoshin da Ya bayar lokacin yana raye yau sama da shekaru talatin.
Daga birnin Qum ne Cibiyar da ke kula da harkokin Kur'ani a Iran Ikna ta watsa labarin cewa: bayan shekaru talatin da rasuwar Ayatullah Al'uzma Bujurdi Muhammad Rida Ahmadi Bujurdi shugaban Mu'assisar da ke kula da abubuwan day a bari shi Ayatullahi Bujurdi a wani taron manema labarai ya tabbatar da cewa: wannan littafi da suka fitar ya shafi irin amsoshin day a bayar a fannoni daban-daban na akida da rayuwar dan adam da kuma babu su a cikin risala amaliya dinsa . Har ila yau wannan shi ne karon farko da aka fitar da wani littafi makamancin haka da ya shafi rayuwar marigayi Ayatullah Bujurdi.

388296