IQNA

Wajibi Ne Tsarin Koyar Da Addinin Musulunci Ya Zama Na Zamani

Bangaren kasa da kasa: Ministan kula da harkokin addini na kasar Malazia ya bayyana cewa; dole ne a samar da canji wajen koyar da ilmomin addinin musulunci da daidai da zamani, maimakon dogara da hanyoyin da aka jima an amfani da su wajen koyarwa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Barnama cewa; ministan kula da harkokin addini na kasar Malazia ya bayyana cewa; dole ne a samar da canji wajen koyar da ilmomin addinin musulunci da daidai da zamani, maimakon dogara da hanyoyin da aka jima an amfani da su wajen koyarwa. Ministan ma'aiktar kula da harkokin addinin ta kasar Malazia ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban taron ilimi mai zurfiwanda aka gudanar a kasar, inda ya bayyana cewa bisa la'akari da canjin zamani da kuma ci gaban da zamani ya kawo, ya zama wajibi a yi amfani da hanyoyi na zamani wajen koyar da ilmomi na addini, kamar yin amfani da na'ura mai kwakwalwa da dai dai sauran hanyoyi da nufin saukaka koyon ilimin.

388918