Bnagaren siyasa da zamantakewa: Ma'aikatar kula harkokoin bunkasa tattalin arziki ta kasar Jordan, ta mika wani taimako ga cibiyar gudanar da ayyukan taimako ta kasar domin mika taimakon nata ga al'ummar Gaza.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga jaridar Ra'ayi da ake bugawa a kasar Jordan cewa; ma'aikatar kula harkokoin bunkasa tattalin arziki ta kasar Jordan, ta mika wani taimako ga cibiyar gudanar da ayyukan taimako ta kasar domin mika taimakon nata ga al'ummar Gaza. Ministan ma'aikatar kula da harkokin bunkasa tattalin arziki ta kasar Jordan Halu Laduf yayin da yake mika taimakon ga cibiyar kula da hrakokin bayar da agaji ta kasar ya bayyana cewa; an hada wannan taimako ne da nufin taimaka ma al'ummar gaza da suka fuskanci munanan hare-haren rashin imani daga yahudawan sahyuniya a cikin farkon shekarar nan, kuma wannan a cewarsa somin tabi ne, al'ummomin kasar Jordan za su ci gaba da yin duk abin da za su iya wajen taimaka ma 'yan uwansu palastinawa musamman ma mazauna zirin Gaza.
389095