IQNA

Palasdinawa Sun Yi Zanga-Zangar Wadai Isra'ila Da Matakin Da Ta Dauka Kan Masallacin Kudus

Bangaren kasa da kasa; daruruwan palasdinawa ne suka gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da Haramtacciyar kasar isra'il kan kokarinta na maida masallacin na yahudawa da yahudanci.
Bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta kasar Koweiti KUNA Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ta watsa rahoton cewa: wannan zanga-zangar nuna rashin jin dadi da matakin da gwamnatin Yahudawan sahayoniya ke dauka kan masallacin Kudus mai tsarki da kokarin rusa shi da kuma maida shi ya zama na yahudawa da yahudanci .Yan Sandan Haramtacciyar kasar Isra'ila sun dauki matakan tsaro kaukaura da hana zirga –zirga a kusa da masallacin na Kudus domin hana wannan zanga-zanga amma ina Palasdinawa da daman gasket ne suka fito domin halartar wannan zanga-zanga ta nuna bacin rai.

389685