Bangaren Adabi : cibiyar da ke kula da yada al'adun musulunci a markadin Radawi Mai girma ta dauki dawainiyar gudanar da wannan aiki mai matukar muhimmanci.
Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a Iran Ikna ce ta nakalto majiyar hulda da jama'a ta markadin Imam Rida (AS) da ke birnin Mashhad ta watsa rahoton cewa: wannan littafi a shekara ta 1379 ne aka shigar da shi a kasuwa karkashin wata cibiya da ke aiki da abubuwa na tarihi kuma wannan shi ne karo na biyu da aka buga shi sai kuma wannan karo da aka fassara shi a cikin harshen Turancin Ingilishi domin bawa masu ma'amala da wannan harshe damar amfanuwa da kuma sanin wannan bawon Allah da yadda Imam Sajjad (AS) Ya rayu tun daga ranar Haifuwarsa har zuwa lokacin day a yi shahada da bangarorin day a shafi rayuwarsa ta hanyar ma'anawiya,zamantakewa, siyasa,ilimi da saninsa.
390046