Bangaren kasa da kasa: Za a gudanar da gasa kan masaniya dangane da addinin musulunci a birnin North Branzvic da ke Amurka.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na Muslim Voice cewa; Za a gudanar da gasa kan masaniya dangane da addinin musulunci a birnin North Branzvic da ke Amurka. Bayanin ya ci gaba da cewa msnufsr gudsnsr da gasar dai ita ce karfafa gwiwar matasa da kuma kanan yara musulmi wajen samun masaniya kan addinin msulunci musamman ma tarihinsa da kuma al'adunsa. Wannan dai shi nekaro na goma sha daya da ake gudanar da irin wannan gasa a Amurka, wanda babbar cibiyar kula da harkokin addinin musulunci ta Amurka ke daukar nauyin shiryawa da gabatarwa. An fara gudanar da irin wannan gasa ne tun a cikin shekara ta 1999, kuma har yanzu ana ci gaba da gudanar da ita a kowace shekara.
390376