IQNA

Kungiyar PLO Da Sauran Kungiyoyin Gwagwarmaya Asalinsu Daya Ne

Bangaren siyasa da zamantakewa: Babban malamin addinin nan na kasar Labanan Allamah sayyid Muhammad hussain Fadlollah, ya bayyana cewa; kungiyar PLO da sauran kungiyoyin gwagwarmayar palastinu da na Labanan asalinsu daya ne, kuma dukkaninsu bangarori ne masu matukar muhimmanci.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; babban malamin addinin nan na kasar Labanan Allamah sayyid Muhammad hussain Fadlollah, ya bayyana cewa; kungiyar PLO da sauran kungiyoyin gwagwarmayar palastinu da na Labanan asalinsu daya ne, kuma dukkaninsu bangarori ne masu matukar muhimmanci. Allamah Fadlollah ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da hudubar sallar juma'a ta wannan mako, inda ya tabbatar da cewa gwagwarmayar al'ummomin Labanan da Palastinu abubuwa ne guda biyu dab a za a iya raba su ba, domin kuwa dukkanin bangarorin biyu suna gwagwarmaya ne domin kare karamar al'ummominsu.

390068