Bangaren rahoto: Shugaban cibiyar kula da yada koyarwar addinin Musulunci ta kasar Iran Abbas Ali fatemi ya bayyana cewa; cibiyar ta tanadi bayanai da dama da tattara dangane da muhimmancin lakabin da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya baiwa wannan shekara ta Iraniyawa, kuma za ta raba su nan ba da jimawa ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; shugaban cibiyar kula da yada koyarwar addinin Musulunci ta kasar Iran Abbas Ali fatemi ya bayyana cewa; cibiyar ta tanadi bayanai da dama da tattara dangane da muhimmancin lakabin da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya baiwa wannan shekara ta Iraniyawa, kuma za ta raba su nan ba da jimawa ba. Ya ci gaba da cewa babbar manufar hada wadannan bayanai da suka hada jawaban da shi kansa jagoran juyin juya hali ya gabatar kan hakan, da ma wasu jawabai da jami'ai suka gabatar dangane da muhimmancin wannan suna da aka baiwa shekarar, shi ne samar da wani yanayi na tattali tsakanin al'umma, tare da rage almubazzaranci a cikin lamurra nay au da kullum.
390185