IQNA

Za A Gudanar Da Taro Kan Sulhu Da Adalci A Cikin Littafai Masu Tsarki

Bangaren fikra da ilimi: Za a fara gudanar da taro na kasa da kasa kan sulhu da adalci a cikin littafai masu tsarki da mahangar masana falsafa a kasar Tunisia.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; za a fara gudanar da taro na kasa da kasa kan sulhu da adalci a cikin littafai masu tsarki da mahangar masana falsafa a kasar Tunisia. Rahoton ya ci gaba da cewa wannan taro zai samu halartar masana daga kasashe daban-daban, da suka hada kasashen Iran, Masar, Faransa, Algeria, Morocco da kuma mai masafkin baki Tunisia. Masanan za su tattauna kan mahangar littafai masu tsarki da aka safkar daga sama kan adalci da sulhu da kuma ma'anarsu, kamar yadda za su yi dubi dangane da mahangar falsafa kan adalci da sulhu. Za a karanta bayanin babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon a wajen taron.


390877