Bnagaren fikira da ilimi: Shugaban cibiyar kula da rubuce-rubucen mashhurin malamin nan Allah Kulaini dangane da fikihun musulunci, ya bayyana cewa an fitar da wasu bayanai dangane da rubuce-rubucen Allamah Kulaini.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga bangaren yada labarai na babbar cibiyar bincike kan rubuce-rubucen magabata ta kasar Iran cewa; shugaban cibiyar kula da rubuce-rubucen mashhurin malamin nan Allah Kulaini dangane da fikihun musulunci, ya bayyana cewa an fitar da wasu bayanai dangane da rubuce-rubucen Allamah Kulaini. Ya ci gaba da cewa bias la'akari da gagarumar gudun mawar da babban malamin ya bayar wajen yada ilimin addinin musulunci musamman ma a bangaren fikihu, ya sanya cibiyar ta bayar da dama ga masu bincike da su yi nazari kan rayuwarsa da kuma rubuce-rubucensa, inda za a bayar da kyautttuka na musaman ga wadanda suka yi hakan, kuma tuni aka fara tattara bayanai da makaloli dangane da rubuce-rubucensa da kuma tarisinsu a cikin al'ummar musulmi.
392885