Bnagaren fikira da ilimi: An gabatar da wata makala mai taken uhimmancin hadin kai tsakanin al'ummar musulmi, wadda Ikbal Lahuri ya rubuta, Wadda za a fitar da ita a taron kasa da kasa da za a gudanar a Istanbul na Turkiya kan rubuce-rubucensa.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; an gabatar da wata makala mai taken uhimmancin hadin kai tsakanin al'ummar musulmi, wadda Ikbal Lahuri ya rubuta, Wadda za a fitar da ita a taron kasa da kasa da za a gudanar a Istanbul na Turkiya kan rubuce-rubucensa. Shugabancin cibiyar gudanar da bincike kan rubuce-rubucen Ikbal Lahuri kuma mamba kwamitin bincike kan harkokin ilimi na jami'ar Allamah Tabatabai Tamim Dari shi ne ya fitar da wannan makala daga cikin jerin wasu makaloli na Ikbal Lahuri, dangane da muhimancin da ke tattare samun hadin kai tsakanin al'ummar musulmi na duniya. Kuma za a buga wannan makala domin rabata a taron kasa da kasa da za a gudanar a birnin Istanbul na kasar Turkiya kan rubuce-rubucensa. Tamim Dari dukkanin abubuwan da makalar ta kunsa na nuni da mahangarsa kan hadin kan musulmi.
392886