Bangaren kasa da kasa: Cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar saudiyya ta kirkiro da wata hanyar koyon karatun kur'ani mafi sauki ta hanyar internet, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da aka kirkiro da irin wannan hanya.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya nakalto daga shafin internet na kamfanin dillancin labaran Misrion cewa; cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar saudiyya ta kirkiro da wata hanyar koyon karatun kur'ani mafi sauki ta hanyar internet, wanda kuma wannan shi ne karo na farko da aka kirkiro da irin wannan hanya. Bayanin ya ci gaba da cewa cibiyar ta gudanar da wannan aiki ne domin sawake yawan ayyukan da take gudanarwa, ta yadda ayyuka da daman a koyar da kur'ani za a iya aiwatar da su cikin sauki ta hanyar internet. Shugaban cibiyar ya ce yanzu haka suna da dalibai matasa maza 2900 da kuma dalibai 'yan mata 2800 da suke koyon karatun kur'ani, gami da harda da kuma sanin ka'idojin karatun kur'ani mai tsarki.
392175