IQNA

Jagoran Mabiya Addinin Kirista A Kuwait Ya Yi Kira Zuwa Ga Zaman Lafiya

Bangaren fikira da ilimi: Jagoran mabiya addinin kirisata akasar Kuwait ya yi zuwa ga zaman lafiya tsakanin dukkanin al'ummomi da mabiya addinai a fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Anba cewa; babban jagoran mabiya addinin kirista a kasar Kuwait ya yi ga dukkanin al'ummomi na duniya da ma mabiya addinai daban-daban a ko'ina cikin da su zauna lafiya tare da fahimtar juna, da kuma girmama addinin kowane daya bangare. Ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a birnin Kuwait fadar mulkin kasar da ked a dangantaka da addinin kiristanci, wanda ya samu halrtar baki da dama, da suka hada jakadun kasashen duniya da ke kasar ta Kuwait, gami da wakilan kasashen larabawa da ma wadanda ban a larabawa ba, da kuma manyan 'yan kasuwa da suke zaune a kasar Kuwait, ya bayyana fatan samun zaman lafiya mai dorewa a kasashen Labanan palastinu da kuma Iraki.

392149