Bangaren siyasa: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran bisa dogaro da wani rahoto ya bayyana cewa Saudiyya na ci gaba da bayar da takardun izinin shiga kasarta ga Iraniyawa masu zuwa aikin Umrah da kuma ziyara ba tare da samun wani cikas ba.
Kamfanin dillancin labaran Ikna ya habarta cewa; a wata zantawa da ta hada shi da manema labarai a jiya a birnin Tehran kakakin ma'aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran bisa dogaro da wani rahoto ya bayyana cewa Saudiyya na ci gaba da bayar da takardun izinin shiga kasarta ga Iraniyawa masu zuwa aikin Umrah da kuma ziyara ba tare da samun wani cikas ba. Hassan Kashkawi ya ci gaba da cewa a cikin wani rahoto da ya samu daga ofishin jakadancin Iran da ke kasar Saudiyya, jami'an huldar diplomasiyar Iran da ke kasar suna kokarin ganin an samu gagarumin canji a harkar bayar da izinin shiga kasar Saudiyya ga Iraniyawa, ya ce amma dai har yanzu Saudiyya din tana bayar da izinin bisa ka'adojinta na da, amma a cewarsa hakan ma babu laifi, sai dai kawai suna bukatar a kara kyautata lamarin ne.
395393