Bangaren kasa da kasa: An gudanar da wani taro kan tarihin ma'aiki a birnin Birgin na kasar Amurka, wanda cibiyar kula da addinai ta birnin New York na kasar Amurka ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran ikna ya nakalto daga shafin internet na yeniasya cewa; An gudanar da wani taro kan tarihin ma'aiki a birnin Birgin na kasar Amurka, wanda cibiyar kula da addinai ta birnin New York na kasar Amurka ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa. Daya daga cikin jagororin musulmi a kasar Amurka day a halarci wurin taron Muhammad Amin Awaiz ya bayyana cewa taron ya kayatar matuka, domin kuwa sun yi amfani da wannan damar wajen bayyana cikakken tarihin manzon Allah SAW kamar yadda yake a cikin addinin musulunci, sabanin yadda wasu marubuta a kasashen turai ke kokarin gurbata tarihinsa domin nisantar da mutanen kasashensu daga addinin musulunci. Ya ce idan da dukkanin al'ummomin duniya za su koyi da irin rayuwar ma'aiki da sun zauna lafiya.
396190